23/09/2022
GEMU SIFA CE DAGA CIKIN SIFFOFIN MANZON ALLAH KUMA YAYI UMARNI DA ABAR GEMO A KWASHE GASHIN BAKI
Gemu siffa ce ta musulunci, manzon Allah ya kasance gemunsa ya sauka har kirjinsa, sahabbai s**a ce mun kasance muna gane karatun manzon Allah ta motsin gemunsa (Sallolin azahar da la'asar).
Duk magabata na kwarai da s**a biyo bayan sahabbai sun kasance masu cika gemu. Tara gemu umarni ne na manzon Allah da yace -A cika gemu a rage/aske gashin baki-.
Annabawa ma siffarsu ce tara gemu, shiyasa sanda Annabi Musa ya tafi ganawa da Ubangiji bayan ya dawo sai ya tarar da mutanensa suna bautar dan maraki, cikin fushi ya durfafi Annabi Haruna ya rike gemunsa yana jijjiga shi.
Duk gemun da za'a rike ba karamin gemu bane!
Aske Gemu Haramun Ne A Musulunci Idan Batareda Wani Dalili Na Shariya Ba
Aske gemu tatas siffa ce ta yahudawa Da' nasara!!
Barin Gashin Baki Kazantane Kuma Sifa Ce Daga Yahudawa Da' Nasara!!
Sabida Haka Baya Daga Cikin Dabi'a na Gari Ace Malamin SUNNAH Kuma Mai Waazi Yadinga Aske Gemu Idan Batareda Dalili Na Shariya Ba
Nana Aisha Tace Gemu Ado Ne Ga Maza
Allah Ubangiji yabada Ikon Tsayar Da' Gemu Wanda Basudashi kuma Allah Ubangiji yabashi